Wednesday, 24 October 2018

Amsar da Nafisa Abdullahi ta baiwa wani da yace ta bar shirin fim ta yi aure ta dauki hankula

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta gamu da shawarar wani bawan Allah da ya bata akan sana'arta da kuma yin aure, saidai a wannan karin amsar da ta mayar mishi ba me zafi bace, ta ma baiwa wasu mamaki.


Nafisar dai tana kan tallata sabon fim dinta ne me suna, Yaki a Soyayya.

Shi kuwa wannan bawan Allah sai yace, dan Allah a daina takura mana da wannan kayan shashancin, da kinyi aure yafi Alkhairi da wannan aiki talan kai.

Nafisa kuwa sai ta bashi amsar cewa, Tun dadai ka zo nan, je ka kalli tallar Yaki a Soyayya.

No comments:

Post a Comment