Monday, 8 October 2018

An bayyana dabarar da Atiku yayi amfani da ita wajan cin zabe da kuma daga inda zai dauko mataimakinshi

Rahotanni sun bayyana akan dabarar da Atiku Abubakar yayi amfani da ita wajan lashe zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP. Da ya lura manyan jam'iyyar, musamman a johohin da PDP ke da gwamnoni basa yinshi sai ya fito da dabarar bayar da karfi sosai a jihohin da PDP bata da gwamnoni.


Jaridar Punch ta bayyana cewa, duk da haka Atikun be bar jihohin da PDP din ke mulki ba, yayi kokari ya yagi rabonshi a kusan ko wace jiha.

Jim kadan da lashe zaben nashi ne sai aka fara maganar wanene zai dauka a matsayin abokin tafiyarshi wanda zai zamar mai mataimakin shugaban kasa.

Jaridar ta ruwaito cewa, yankin kudu maso gabas na, Inyamurai sun wa Atiku ruwan kiri'u wanda ana ganin hakan ya taimaka sosai wajan nasarar tashi, sannan kuma daga yankinne ake tsammanin zai dauki mataimaki da zasu yi tafiya tare.

Majiya me karfi a jam'iyyar PDP ta bayyana cewa, daga jihohin Abia ko Ebonyi ne Atikun zai dauki abokin tafiya. 

No comments:

Post a Comment