Sunday, 7 October 2018

An Bude Gasar Al-Qur'ani Mai Girma A Masallacin Manzon Allah

A kokarin ta na zaburar da dalibai haddan Al-qur'ani mai girma, masarautar Saudiyya, a jiya Asabar ta kaddamar da gasar karatun Al-qur'ani mai girma a karo na 40 a masallacin Manzon Allah SAW dake birnin Madina.


Wannan dai shine karo na farko da kasar Saudiyya zata gudanar da gasar a cikin masallacin. Zaqaqurai daga kasashe daban daban a fadin duniya ne zasu gwabza a gasar.

Kasar Saudiyya dai ta saba shirya irin wadannan gasa, inda ake karrama wadanda suka yi nasara da kyaututtuka na karamci, kana har da daukan nauyin karatun su. 

Kasar saudiyya ta bayyana Gasar mai taken "Gasar Haddar Karatun Alkur'ani Maigirma Da Tafsirinsa Na Duniya Na Sarki Abdul'aziz" a matsayin hanya na hidimtawa da kiyaye Alkur'ani mai girma.

Kazalika kasar, na daga cikin manufofin ta karfafa yaran musulmai komawa ga littafin Allah SWT ta hanyan haddace shi da iya tafsirin sa da tadabburin sa.

Masu bukatar ganin gasar suna iya bin link din nan kai tsaye a YouTube:
 https://m.youtube.com/watch?v=KIa23qGEH8A
Rariya.

No comments:

Post a Comment