Friday, 12 October 2018

An bukaci jami'an tsaro su rage yin fara'a

An bukaci jami'an 'yan sanda a filayen jiragen sama na Indiia sama su rage sakin fuska.
Hukumomin tsaro sun bayyana fargabar cewa sakin fuska na iya haifar da matsala ga tsaro da kuma barazanar ta'addanci.


Hukumar kula da tsaron tashohin jiragen sama a Indiya tana son ne jami'anta su mayar da hankali sosai ga tsaro maimakon sakin fuska ga mutane da nuna sanayya.

An bayyana cewa hukumar na ganin sakin fuska da yawa da kulla abota hatsari ne ga tsaron tashoshin jiragen sama.

Shugaban hukumar ya ce ta haka ne aka yi amfani aka kai harin 9/11 a Amurka.
An bukaci jami'an tsaron a India su sauya yanayin mu'amularsu da mutane.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment