Thursday, 11 October 2018

An cire kuri'ar jin ra'ayin wanda zai lashe kyautar Ballon d'Or bayan da Messi da Salah suka fi yawan kuri'u

Masu shirya bayar da kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta Ballon d'Or sun bayar da dama ta yanar gizo ga masoya kwallon kafa da su zabi wanda suke tunanin shine ya fi cancanta ya lashe kyautar ta kakar wasan 2017/18, bayan kada kuri'u sama da dubu dari 700 dan wasan Barcelona, Lionel Messi da na Liverpool, Mohamed Salah ne suka fi yawan kuri'u, nan da nan kuwa sai aka cire zaben daga shafin yanar gizon Magazine France Football.


Messi dai ya lashe kashi 48 na kuri'un da aka kada sannan sai Mohamed Salah ya lashe kashi 31 sai Ronaldo ne ya zo na Uku.

Mutumin da ake ta wa tsammanin zai lashe gasar, Modric bai samu wata kuri'ar azo a gani ba kamar yanda Marca da The Sun suka ruwaito.

Cire wannan zabe daga yanar gizo ya batawa masoya kwallon kafa rai sosai inda aka yi ta sukar masu shirya bayar da kyautar da nuna fifiko.

'Yan jarida ne dai da wasu mahukunta kwallon kafa ke da alhakin tantance wanene zai lashe kyautar A karshe.

No comments:

Post a Comment