Saturday, 13 October 2018

An dawo da fasa bututun mai a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya sun ce akalla mutane 19 suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon fashewar wani bututun mai a wasu kauyuka guda biyu dake jihar Abia.


Shugaban hukumar tsaro ta Civil Defence a Jihar, Benito Eze yace cikin mutanen da suka mutu akwai mace guda, kuma hadarin ya faru ne da misalign karfe 2.47 na daren jiya Alhamis.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewar ana fargabar akwai sojoji 2 da hadarin ya ritsa da su.

Fasa bututun mai ana satar mai dai ba wani sabon abu bane a sassan Najeriya.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment