Tuesday, 9 October 2018

An ga wani gwamnan Arewa na karbar cin hanci

Wannan abin kunya dame ya yi kama?
Jaridar Daily Nigeria ta bankado asirin wani gwamna a yankin mu na Arewa maso yammacin kasar nan, yana ta karbar cin hancin miliyoyin daloli, na cin hancin da 'yan kwangila ke bashi.


Wannan gwamna dama ya yi kaurin suna wajen karbar rashawa, duk da cewar har iyalansa sukan shiga zargi kan yadda ake bi ta kansu domin samun Oga, amma yanzu bayyanar wannan fefen bidiyo ya fasa kwai kuma na tabbata an bude sabon shafi dangane da yadda kulba ke barna ana cewa jaba ce. 

Kwararru a fannin sanin siddabarun hotuna dai sun yi nazarin wannan bidiyo sun kuma tabbatar da cewar tabbas babu algus cikin tsagwaron gaskiyar wannan abin kunya. Yanzu haka ma wannan abin fallasa zai kawo nakasu matuka ga takarar wannan gwamna wanda ke kokarin yin tazarce a jiniya karo na biyu.

 Wannan fefen bidiyo ya nuna gwamnan sanye da babbar riga da hula a cikin ofishinsa ana mika masa daloli yana amsa yana turmutsa su cikin babban riga. 

Babban abin takaicin shine yadda wasu ke mayar da ofishin gwamnati tamkar rumfar kasuwa ta yadda za su rufe ido daga wahalar da talakawa ke sha, su kuma suna wawashe lalitar talakawan.

No comments:

Post a Comment