Saturday, 20 October 2018

An gano inda shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya ke buya

Bayan watanni da masu yawa ta bacewarsa, an gano shugaban haramtaciyar kungiyar masu fafutikan neman kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kani a birnin Jerusalem da ke kasar Isra'ila a jiya 19 ga watan Oktoban 2018.

Hotuna da bidiyon Nnamdi Kanu yana bauta a Jerusalem sun karade kafafen sada zumunta bayan Radio Biafra da wallafa hotunan da bidiyon.

Kanu dai ya bace ne a watan Satumban 2017 bayan sojojin Rundunar Phython Dance sun kai wata farmaki gidansa.
Bayan bacewarsa mutane da kungiyoyi daban-daban suna ta korafi cewar gwamnatin tarayya ne da boye shi amma kuma babu wata hujja da ke nuna hakan.

Wasu kuma na ganin ya tsere ne saboda haramcin da gwamnati ta yiwa kungiyar nasa bayan an ambata kungiyar a matsayin kugiyar ta'addanci.
Nnamdi Kanu da 'yan kungiyarsa sun sha yiwa gwamnati barazanar cewa za su tayar da hankalin al'umma kuma su hana a gudanar da zabe a wasu jihohin kudu muddin gwamnatin tarayya ba ta amince da ba su ikon kafa kasarsu ba.
Legit.ng

No comments:

Post a Comment