Wednesday, 3 October 2018

An gano mota ta 3 a rafin da aka gano motar sojan nan da yayi batan dabo: Sojoji sun bayyana abinda zai faru da mutanen garin


Sojoji sun samu mota na uku kirar Saloon mai dauke da namba kamar haka Bauchi-AG 645 TRR daga cikin kududdufin da aka samu motar Janar Idris Alkali a kauyen Dura-Du.Janar Idris Alkali me ritaya ya batane ranar 3 ga watan Satumba a lokacin da yake kan hanyarshi ta zuwa mahaifarshi ta dake jihar Bauchi.

Bayan motar Janar Idris da aka gano an kuma gano wata motar Bas da direbanta sannan kuma ga mota ta uku da aka sake ganowa.

Da yake hira da manema labarai, majo janar, Augustine Agundu, kwamandan Operation Safe Haven yace, matuka mota na yankin sun bayyana musu cewa akwai karin motoci 3 a cikin rafin kuma ba zasu gaza ba sai sun fito da dukansu.

Da aka tambayi Maj.-Gen. Benson Akinruluyo, kwamanda na 3 Division, Rukuba, akan cewa mutanen kauyen suna cikin fargabar wane hukunci sojoji zasu dauka a kansu.

Sai yace, kada su tayar da hankalinsu, sun gano motar Majo Idris Alkali kuma an basu umarnin su gano shi ko a mace ko a raye, dan haka mutanen kauyen zasu iya gaya musu inda suka ajiyeshi ko kuma gawarshi. Ya kara da cewa, ba zasu daina bincike ba sai sun gano shi ko kuma gawarshi, kamar yanda shafin Tori ya ruwaito.No comments:

Post a Comment