Monday, 1 October 2018

An gano silalla 864 a cikin wani mutum

Likitoci a kasar Japan sun fidda sulalla dubu 864 wanda nauyinsu ya haura kilo 8 daga cikin wani marar laifiya mai shekaru 51 da haihuwa.


Marar lafiyan ya share shekaru 30 yana fama da gajiya,bakin ciki,rashin abinci da kuma gajiyar fitar hankali.Abinda yasa ya garzaha asibiti mafi kusa.

Bayan sun dauki hoton cikinsa,sai likitoci suka gano wasu ababe a cikin cikinsa,wanda hakan yasa suka yanke shawarar yi masa tiyata na take.

Fede tumbinsa ke da wuya,sai suka gano sulalla dubu 894,000 burjik a cikinsa.

Kudaden sun hada da sule na Yen (Kudin Japan) 1,sama da dari, sulalla na Yen 5 su 99,sulalla na Yen 10 su dubu 642,sulalla na Yen 50 su 8 da kuma sulalla na Yen 100 su 5.

Wani bincike mai zurfi da kwararrun likitoci suka gudanar bayan tiyatar,ya nuna cewa marar lafiya ya kamu da cutar "Pika",wacce ke tilasta wa mai ita hadiyar ababen kamar su,alli,gashi,takarda da kuma sulalla.

An mika majinyacin hannun likitocin kwakwalwa sakamakon tabin hankalin da yake fama da shi.

Pika,cuta ce da ke taba kwakwalar matasa a lokacin balaga,yara kanana da mata masu juna-biyu.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment