Saturday, 13 October 2018

An Gudanar Da Zikiri Tare Da Yi Wa Kasa Addu'a A Masarautar Kano

Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ll,  ya jagoranci mabiya ɗariƙar Tijjaniya domin gudanar da zikirin shekara da addu'o'i kamar yadda aka saba yi duk shekara, kuma taron zikirin na bana ya mamu halartar manyan shugabanni da Malaman ɗarikar Tujjaniyya wanda aka yi a fadar masarautar Kano.Kuma mai girma mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusif Nasiru Yusuf Gawuna, shi ne ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa wajen babban zikirin.

Allah ya jaddada rahama ga magabatan mu, ya saka musu da alheri, ya karawa zuriyar gidan Dabo albarka, ya gafartawa Sarki Ado Bayero, Allah ya taimaki Mai Martaba Sarki Sanusi ll ya ja zamanin sa, Amin.
Rariya.

No comments:

Post a Comment