Tuesday, 16 October 2018

An kusa bawa hammata iska tsakanin kakakin Buhari da na Atiku

Da safiyar jiya, Litinin ne, aka yi wata mahawara mai zafin gaske tsakanin kakakin kwamitin kamfen din Buhari, Festus Keyamo, da na kwamitin yakin neman zaben Atiku, Segun Sowunmi.

Mahawara ta yi zafin gaske har ta kai ga rikidewa zuwa musayar kalamai ma su zafi da ta kusa kai wa ga bawa hammata iska.


Keyamo da Sowunmi sun ki yin shiru domin bawa dan jaridar gidan talabijin na Channels damar yi masu tambayoyi, lamarin da ta kai ga gidan talabijin din ya katse shirin ba tare da kammala shi ba.

Wannan mahawara mai zafi ta faru ne da safiyar yau a wani shiri da gidan talabijin din na Channels ke nunawa kai tsaye.

Tun bayan da Atiku ya lashe zaben cikin gida na jam'iyyar PDP ake musayar yawu tsakanin magoya bayansa da na shugaban Buhari, dan takarar APC.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment