Saturday, 13 October 2018

An nada sabon Dan Masanin Kano

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya nada sabon Dan Masanin Kano shekara guda bayan rasuwar Alhaji Yusuf Maitama Sule Dan Masanin Kano na farko.


Sarkin ya nada Alhaji Abdulkadir Maitama Sule, da aka fi sani da Hakimi a matsayin sabon dan masanin Kano, a ranar Juma'a a fadarsa.

Wannan ne dai karo na biyu da aka nada sarautar ta Dan Masani a Kano, inda Dr Yusuf Maitama Sule shi ne aka fara ba wa sarautar wacce aka aro ta daga masarautar Katsina.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na daya wanda ya yi sarauta tsakanin 1953-1963 shi ne ya fara bai wa Yusuf Maitaiam Sule sarautar ta Dan masani.

Tsohon Dan masanin na Kano ya rasu ne a watan Yulin 2017 bayan gajeriyar rashin lafiya.

Wanene sabon Dan Masanin Kano?

Mai martaba Sarkin Kano ya bar sarautar ta Dan Masani a gidan Alhaji Yusuf Maitama Sule, a cikin 'ya'yansa.

Abdulkadri shi ne karamin da namiji a cikin 'ya'yan marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule.

An haife shi a watan Yunin 1967 a birnin Kano.

Ya yi makarantar firamare da sikandare a Kano, sannan ya halarci makarantar Kaduna Polytechnic.

Gabanin nada shi a matsayin Dan Masani, Alhaji Abdulkadir shi ne yake rike da sarautar Turakin Madakin Kano, sarautar mahaifin Alhaji Yusuf Maitama Sule, wato kakan sabon Dan Masani.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment