Sunday, 14 October 2018

An saki bidiyon dake zargin gwamnan Kano da karbar cin hanci daga hannun 'yan kwagila: Gwamnatin Kano ta mayar da martani

Shafin Daily NIgerian ya wallafa hotunan Bidiyonnan da ya fada cewa yaga gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje na karbar cin yancin dala miliyan 5 daga hannun 'yan kwangila, me shafin Jafar Jafar ya fada a baya cewa yana da biyon saidai saboda barazanar da yake samu akan labarin, yana so ya samu guri me kyau da zai zauna da iyalinshi kamin ya wallafa su.Ga hoton bidiyon:
Sai dai bayan wallafa hoton bidiyon, gwamnatin jihar Kano ta hannun kwamishinan labarai matasa da al'adu, Malam Muhammad Garba tace za ta shigar da kara akan mawallafin jaridar bisa zargin bata suna da yawa gwamnan Kano.

Sanarwar ta kara da cewa hoton bidiyon an tsara shine kawai dan a batawa gwamnan Kano din suna da kuma rage mai farin jini a gurin jama'ar jihar Kano da kuma ragewa jam'iyyar APC yawan kuri'un da zata samu a babban zabe na shekarar 2019 me zuwa.

Sanarwar ta kara da cewa babu kanshin gaskiya a tattare da abinda wannan bidiyo ya kunsa kuma ba zai dauke wa gwamnatin jihar hankali ba kan ayyukan raya kasa da takewa al'umma. A karshe sanarwar ta yi kira ga mutanen jihar 'yan APC da su kwantar da hankulansu su zama masu bin doke da oda.

No comments:

Post a Comment