Monday, 29 October 2018

An sako El-Rufa'i a gaba a kan kalaman tashin garin Gonin Gora

Malaman addini da sarakunan gargajiya sun sako gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Elrufa'i, a gaba bayan ya yi barazanar tashin garin Gonin Gora.


A ranar Asabar da safe ne gwamna El-Rufa'i yayin wani shiri da aka yada kai tsaye, ya yi barazanar tashin garin Gonin Gora, da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, bisa yadda su ke tare hanya da kashe mutane duk lokacin da rikici ya barke a garin Kaduna.

Sai dai shugabannin al'umma a yankin sun nuna matukar mamakinsu bisa furucin gwamnan tare da yin kira ga jama'ar su da su zama ma su biyayya ga doka.

Da yake magana da manema labarai, Akila Luka, Sarki Samarina, ya bukaci jama'ar na Gonin Gora da su zama ma su biyayya ga doka da kaunar zama lafiya.

Kazalika ya bayyana mamakinsa bisa yadda gwamnan ya gaza yin irin wannan barazana ga mutanen yankin Mando, Nasarawa, Badiko, Anguwan Muazu, Panteka da su ma ke tare hanya da kashe mutane duk lokacin da rikici ya tashi.

A nasa bangaren, Shekwolo Ayuba, shugaban kungiyar kiristoci (CAN) a karamar hukumar Chikun, ya bukaci jama'ar yankin su zama ma su son zaman lafiya tare da bayyana cewar za su jira su ga mai gwamnan ke nufi da da kalaman cewar zai rushe garin.

Garin Gonin Gora da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja na da yawan mutane kimanin 800,000, dukkansu mabiya addinin Kirista.
Legit.ng.


No comments:

Post a Comment