Wednesday, 3 October 2018

An samu fargabar aukuwar aman wuta daga duwatsu a Abuja

Mazauna yankin Mpape dake babban birnin tarayya aun kadu da ganin wani abu me kama da aman wuta da duwatsun yakin ke fitarwa, bayan ganin wannan lamari sunyi gaggawar kiran jami'an gwamnati maau bayar da agajin gaggawa.

Ministan ma'adanai, Abubakar Bawa Bwari da na Abuja, Muhammad Musa Bello da shugaban ma'aikatar kula da yanayin kasa da duwatsu, da sararin samaniya, Alex Ndubuisi Nwegbu karkashin gwamnatin tarayya sun kai ziyara yakin.

Sun bukaci mutanen yakin Mpape da su kwantar da hankalinsu yayin da gwamnati zata binciki lamarin.

Gwamnatin ta kuma basu tabbacin cewa Najeriya bata daga cikin kasashen da aman wuta zai iya faruwa.

An dai dauki samfarin wannan abu da aka gani dan zuwa a yi gwaji.

Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kadan bayan da aka samu rahotannin motsin kasa a Abujar.
DailyTrust.

No comments:

Post a Comment