Tuesday, 23 October 2018

An sassauta dokar hana zirga-zirga a Kaduna


Gwamna jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sanar da sassauta dokar hana fita ta sa'a 24 da aka sanya a jihar ranar Lahadi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Twitter, sai dai ba duka sassan jihar ba ne aka sassauta dokar.

Gwamnan ya fitar da sanarwar ce bayan da aka kammala taron majalisar tsaro ta jihar.

An sassauta dokar a birnin Kaduna, inda a yanzu dokar za ta fara aiki daga karfe 5 na yamma zuwa karfe 1 na rana.

Wannan na nufin kenan mutane za su iya zirga-zirgarsu da harkokinsu a birnin tsakanin karfe 1 na rana zuwa karfe 5 na yamma.

Har ila yau, gwamnan ya ce akwai unguwannin da dokar hana fita za ta cigaba da aiki wadanda su ne Kabala West da Kabala Doki da Narayi da Maraban Rido.

Sanarwar ta kuma ce an rage tsawon awoyin hana fita a yankunan Kasuwan Magani da Kujama, wuraren da rikicin ya samo asali.

A daren jiya gwaman ya sanar da mutanen jihar cewa mutum 5 ne suka rasa rayukansu a rikicin na baya-bayan nan a yayin wani jawabi da yayi ta kafofin watsa labarai.

Amma akwai rahotannin da ke cewa wadanda suka mutu sun kai mutum 26.

Hakazalika ya ce an kama mutane da adama da ake zargi da hannu wajen tayar da rikicin.

Ya kuma ce za a hukunta dukkan wadanda aka samu da laifim tayar da wannan hatsaniyar.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment