Sunday, 28 October 2018

An Sassauta Dokar Hana Zirga-Zirga A Kaduna

Gwamnatin jihar kaduna ta sassauta dokar hana Zirga-Zirga a cikin garin Kaduna inda Jama'a za su ci gaba da zirga-zirga da harkokin a yau Lahadi har zuwa karfe 5 na yamma.


Kakakin gwamnatin jihar, Samuel Aruwa ya ce a gobe  Litinin kuma za a iya zirga-zirga daga karfe 6 na safe zuwa 5 na yamma sai dai kuma dokar hana yawon dare tana nan daram.

No comments:

Post a Comment