Sunday, 14 October 2018

An yi barazanar harbin wani jarumin fim din Hausa da bindiga saboda son Buhari da yake yi

Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello na daya daga cikin jaruman masana'antar da suka fito fili suka bayyana soyayyar su ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kuma sukar Atiku Abubakar.


Bello ya bayyan ta dandalinshi na shafin Twitter cewa saboda soyayyar da yake wa Buhari da kuma sukar Atiku an mai barazanar za'a harbeshi da bindiga.

Saidai ya bayar da amsar cewa shifa na mijine kuma zai dauki alhakin duk wani abu da yayi kuma an haifeshine dan yabi gaskiya ya kuma yaki rashin gaskiya ba tare da la'akarin me zai je ya zo ba.

No comments:

Post a Comment