Friday, 12 October 2018

An yi garkuwa da matashin da ya fi kowa kudi a Afirka

A garin Darussalam na Tanzaniya an yi garkuwa da Muhammad Dewji matashi mafi karancin shekaru da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka.


An bayyana cewar wasu da ba a san ko su waye ba ne suka yi garkuwa da matashin mai shekaru 43 a gaban wani gidan otel.

an kama mutane 3 game da lamarin.

An bayyana cewar bakake da farar fata ne suka yi garkuwa da Dewji da ya ke mutum 1 kadai a Tanzaniya da ya mallaki biliyoyin daloli.

Ministan Muhalli na Tanzaniya January Makamba da yake abokin dan kasuwar ya bayyana tattaunawa daiyayensa kuma sun tabbatar masa da an yi garkuwa da abokin nasa.

Shaidun gani da ido sun ce, masu garkuwar sun kama Dewji tare da saka shi a mota kuma suka dinga harbi a cikin iska.

An bayyana cewar a lokacinda aka yi garkuwar da Dewji babu masu tsaron lafiya a tare da shi.

Mujallar Forbes ta bayyana cewar Dewji yana da tsabar kudi har dala biliyan 1.5 kuma a shekarar 2016 ya ce, zai bayar da kyautar akalla rabin kudin ga kungiyoyin bayar da taimako.

Dewji ya habaka kamfanin gidansu ya zama mai aiki a dukkan nahiyar Afirka inda akalla a kasashen nahiyar 6 ya ke da kamfanonin da ke samar da fulawa, kayan sha, tufafi da kayan abinci.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment