Thursday, 18 October 2018

An yi wa Sadio Mane tiyata a hannu

An yi wa dan wasan gaban kungiyar Liverpool Sadio Mane tiyata a hannu, bayan raunin da ya ji lokacin wasan da ya buga wa Senegal a wannan mako.


Dan kwallon ya koma Liverpool don a duba lafiyarsa gabanin karawar da kungiyarsa za ta yi da kungiyar Huddersfield a gasar firimiya ranar Asabar.

Hakazalika 'yan wasan kungiyar Mohamed Salah da Naby Keita da kuma Virgil van Dijk su ma sun ji raunuka lokacin da suke taka wa kasashensu leda a wannan mako.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment