Monday, 1 October 2018

Anga kayan sojannan da ya bace a jikin wani mutum

Bayan nasarar gano motarsa a wani tafin ruwa mai zurfin gaske dake unguwar Dura Du a karamar hukmar Jos ta Kudu, rundunar soji dake neman Manjo Janar Idris Alkali (mai ritaya) da ya bace tayi nasar cafke wani mutum sanye da kakin janar din.


Bayan rahoton cewar hukumar sojin Najeriya ta gano motar Janar (mai ritaya) a karkashin wani kududdufi dake unguwar Dura Du a karamar hukumar Jos ta kudu, bayan fiye da sati uku ana nemansa.

Manjo Janar Idris Alkali ya bace ne tun ranar 3 ga watan Satumba a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja. Rahotannin da hukumar soji ta tattara sun gano cewar Alkali ya bata ne a karamar hukumar Jos ta kudu.

Babu tabbacin ko gawar Alkali na cikin motar. Sai dai Birgediya Janar Umar Mohammed, shugaban rundunar soji dake farautar neman inda Janar din yake, ya bayyana cewar zasu kwashe ruwan domin tabbatar da gawar Alkali na ciki ko akasin haka.

Tun a ranar 20 ga wata ne, Birgediya Janar Umar Mohammed, shugaban tawagar masu neman Janar Alkali, ya shaidawa gidan talabijin na Channels a yau, Alhamis, cewar sun tura rundunar soji zuwa yankin Dura Du dake karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Filato.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment