Saturday, 6 October 2018

APC na fuskantar barazanar rasa dan takara a Zamfara

A jihar Zamfara ta Najeriya jam'iyyar APC na fuskantar barazanar rasa dan takara a babban zaben da za a yi badi, sakamakon takaddamar da ake yi a kan zaben fid da gwani.


A gobe Lahadi ne wa'adin kammala zaben fid da gwanin don mika wa hukumar zabe 'yan takarar zai cika, sai gashi an samu wata sabuwar baraka tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da hedikwatar jam'iyyar APC ta kasa.

Rikicin ya biyo bayan nadin da uwar jam'iyyar ta sake yi wa Dokta Abubakar Fari, wato shugaban kwamitin da ya soke zaben fid da gwanin da aka fara a makon jiya a matsayin wanda zai jagoranci sabon kwamitin da zai gudanar da zaben da ake sa ran yi a wannan Asabar din.

A tattaunawarsa da BBC Gwamnan jihar Abdul'aziz Yari ya ce ba za su yarda da alkalancin shugaban kwamitin zaben ba, kuma ya kalubalanci shugaban jam'iyyar APC ta kasa Adams Oshiomole.

'Ba mu ga dalilin sake aiko da mutum da tun da fari ya ce babu zaman lafiya a zaben ba, domin tuni ya nuna kasa wa dole a sauya mana shi.'

Abdul' aziz Yari da ke magana a fusace ya ce ba za su lamunci aringizon zabe ba, sannan yace shugaban jam'iyyar APC ta kasa ya yi kadan ya ce zai yi iko a jihar Zamfara don haka indai ba za a musu abinda suke so ba to a manta da batun zabe a zamfara.

Gwamnan ya nuna baya fargabar Zamfara ta tashi babu dan takara tun da shugaban jam'iyyar hakan ya nuna.

'Jam'iyyar APC mu muka haifeta don haka babu wanda ya isa ya yi mana iko ko fitar da mu', inji Abdulaziz Yari.

An dai shafe tsawon kwanaki ana tataburza akan wannan zabe da aka sa ran gudanar da shi a yau Asabar, sai dai da alama hakan zai yi wuya.

Ko da dai jam'iyyar APC ta ce za ta yi kokarin gaba da gudanar da zabukan fitar da gwanin a wasu jihohi da ba a kammala su ba.

Rikice-rikice dai suka sarke wadanan zabukan da aka kasa gudanar da su a wasu jihohin Najeriya.
BBChausa

No comments:

Post a Comment