Monday, 8 October 2018

APC ta cewa Atiku shugabancin Najeriya ba na sayarwa ba ne

Jam'iyya mai mulki a Najeriya APC ta yi wa dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar shaguben cewa, shugabancin kasar ba na sayarwa ba ne.


A wata sanarwa da jam'iyyar APC ta fitar ta yi zargin cewa "tsohon shugaban kasar ya yi amfani da kudi ne wajen sayen kuri'un mambobin jam'iyyar don su tsayar da shi takara.

"Shugabancin Najeriya ba na sayarwa ba ne," in ji APC.

APC ta ce "Atiku wanda hamshakin attajiri ne, ya yi amfani da kudi wajen sayen kuri'u daga wakilan jam'iyyar PDP lokacin zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP wanda aka yi ranar Lahadi."

Sai dai a wata sanarwa da ita ma jam'iyyar PDP ta fitar ta musanta zargin hakan, inda jam'iyyar ta ce "zarge-zargen marasa tushe ba za su taimaki Shugaba Buhari ba."

"Babu kamshin gaskiya a zargin da jam'iyyar APC ta yi cewa wadansu masu neman takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar PDP sun yi amfani da kudi wajen sayen kuri'u lokacin zaben fitar da gwani," in ji sanarwar da ta fito daga PDP.

Jam'iyyar ta APC ta kuma taya Atiku Abubakar Murnar samun nasarar zaben fitar da gwanin da PDP ta yi a jihar Rivers.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment