Wednesday, 3 October 2018

APC ta kori takarar tsohon IG Suleman Abba

Jam'iyyar APC mai mulki ta kori takarar kujerar Sanata da Suleman Abba, tsohon shugaban rundunar 'yan sanda ta kasa, ke yi a jiharsa ta haihuwa, Jigawa.


Sakataren yada labaran jam'iyyar APC na kasa, Yekini Nabena, ne ya sanar da haka yau, Talata, a Abuja.

Tsohon IG, Abba, na takarar neman kujerar sanata mai wakiltar jihar Jigawa ta tsakiya a karkashin jam'iyyar APC.

"Kwamitin tantance 'yan takara na jam'iyyar APC bai amince da takarar Suleiman Abba na neman kujerar sanata a jihar Jigawa ta tsakiya ba," a cewar jawabin Nabena.

Sannan ya kara da cewa, "sunan Suleman Abba da aka gani cikin 'yan takarar da aka tantance domin fafatawa a zaben fitar da dan takara, kuskure ne."

Sai dai ya zuwa yanzu jam'iyyar ta APC ba ta bayyana dalilin soke takarar ta Barista Suleiman Abba ba.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment