Sunday, 21 October 2018

APC ta mayar wa Shehu Sani martani

Jam'iyyar APC ta mayar wa Sanata Shehu Sani martani bayan ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam'iyyar.


Dan majalisar dattawan da ke wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya a jihar Kaduna ta Najeriya ya fice daga jam'iyyar APC mai mulkin ne a ranar Asabar.

Sai dai bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba tukuna.

Jami'in tsare-tsare na jam'iyyar APC Ibrahim Masari ya shaida wa BBC cewa ba su ji dadin matakin da sanatan ya dauka na fita daga jam'iyyar ba.

Sai dai ya musanta zargin da dan majalisar ya yi cewa gwamnoni ne ke juya akalar jam'iyyar.

Har ila yau ya ce a matsayinsu na shugabannin jam'iyyar na kasa suna cikin "tsaka-mai-wuya saboda su ma gwamnoni suna ganin ba ma yi musu yadda suke so."

"Yanzu kuma ga wani yana cewa gwamnoni ke yadda suke so," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: "Matsalar Shehu Sani ita ce uwar jam'iyya ta so ta taimaka masa, aka ce ya shiga zaben fidda gwani amma ya kasa zuwa Kaduna inda aka gudanar da zaben."

"Sai yake tunanin cewa zai zauna daga nan Abuja, a rubuta a ba shi tikitin tsayawa zaben, wanda duk duniya babu wanda zai yi mata wannan."

Daga nan Ibrahim Masari ya ce Shehu Sani ba shi da bakin yin magana saboda dan majalisar bai shiga zaben fidda gwanin da aka yi ba a Kaduna.

Hakazalika ya mayar da martani game da zargin da ya yi cewa akwai rashin adalci wajen gudanar da zaben fidda gwanin.

"Kai da ba ka shiga zaben ba, to wace hujja kake da ita na kalubalantar zaben. Ba ka je ba, ba ka aika ba. Kawai so kake a rubuta a ba ka, hankali ba zai dauka ba," in jishi.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment