Monday, 8 October 2018

APC ta rasa 'yan takara a Zamfara

Kwamitin zabe na uwar jam`iyyar APC daga Abuja ya sanar da cewa jihar Zamfara ta tashi ba ta da ko da dan takara guda, sakamakon rashin gudanar da zaben fiitar da gwani, gabannin cikar wa`adin hukumar zabe na mika sunayen `yan takara.


Hakan ta faru bayan shafe tsawon mako daya ana kokarin gudanar da zaben amma ya citura.

Masu neman takara a Jam`iyyar APC ya kansu ya daure sakamakon sarkakiyar da ke tattare da zaben fitarda gwani a jihar.

Sai dai kuma reshen jam`iyyar da ke bangaren gwamnatin jihar ya yi ikirarin kammala zaben fitar da gwanin tare da sanar da `yan takara.

Shugaban jam`iyyar APC, bangaren gwamnatin jihar Alhaji Lawal Liman Kaura, ya sanar da Alhaji Mukhtar Shehu Idris, a matsayin wanda ya yi nasarar tsaya wa jam`iyyar takarar kujerar gwamna a babban zaben da ke tafe.

Kuma reshen jam`iyyar APCn a jihar dai ya yi ikirarin cewa ya gudanar da zaben ne a ranar Lahadi, har ma ya kammala zabe a wasu cibiyoyin da ba a samu damar yin hakan ba a zaben da aka soke a makon jiya.

Sai dai sabon kwamitin zaben fitar da gwanin da hedikwatar jam`iyyar APC ta tura zuwa jihar ya ce bai samu damar gudanar da zaben ba.

Shugaban kwamitin, Manjo Janar Abubakar Mustapha Gana ya shaidawa BBC cewa abubuwa da dama ne suka kawo cikas ga rashin gudanar da zaben yana mai cewa har cikar wa'adin da hukumar zabe ta diba kwamitinsu bai yi abin da ya kawo shi jihar ba.

An dai shafe wuni guda ana kokarin daidaitawa da masu neman takarar, da nufin cimma maslaha gabannin cikar wa`adin gudanar da zaben fitar da gwanin, amma abin ya ci tura.

Hakan na nufin kuma jihar Zamfara ta tashi ba ta da ko da dan takara guda na kujerun da suka hada da gwamna, da sanata da `yan majalisar wakilai da majalisar dokokin jiha.

Sanata Kabiru Marafa daya daga cikin wadanda suka nemi takarar gwamna ya ce ta kare dole kowa ya hakura ya rungumi kaddara.

Sai dai wasu 'yan takarar na cike da takaicin yanayin da jihar ta shiga.

Baya ga jihar Zamfara, zaben fitar da gwanin jam`iyyar APC dai ya bar baya da kura a jihohin Najeriya da dama, inda wasu da suka nemi takara ke kukan rashin adalci.

Hatta mai dakin shugaban Najeriya, Hajiya Aisha Buhari ta soki lamirin zaben fitar da gwanin a shafinta na Twitter, tana cewa ba a yiadalci ba a wurare da dama.

Sai dai kuma a wani abu mai kamar arashi, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shi kuma murna ya taya dukkan wadanda suka samu nasara, kuma ya bukaci wadanda suka fadi da su rungumi kaddara.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment