Thursday, 11 October 2018

APC tana da 'yan takara a jihar Zamfara>>Oshiomhole

Hukumar Zaben Najeriya INEC ta ce jam'iyyar APC mai mulki ba ta da cancantar tsayar da kowane dan takara a jihar Zamfara a manyan zabukan kasar da za a yi badi.


Aliyu Bello, mai magana da yawun hukumar ya shaida wa BBC cewa dama dai tuni hukumar ta aika wa jam'iyyar wasikar gargadi cewa "muddin ba ta kammala zaben fitar da gwani kafin ranar 7 ga watan Oktoba ba, damarta ta wuce."

Ya ce a halin da ake ciki, jam'iyyar ba ta da wata mafita illa ta tuntubi lauyoyinta.

Sai dai jam'iyyar APC ta mayar da martani, ta hanyar wata wasika da shugaban jam'iyyar Kwamred Adams Oshiomhole ya aike wa sakataren hukumar zaben Okechukwu Ndeche.

Wasikar ta musanta maganar da hukumar zaben ta yi a wasikar da ta aike wa shugaban jam'iyyar APC a ranar 9 ga watan Oktoba, inda ta tuhumi jam'iyyar da rashin aiwatar da zabukan fitar da gwani a jihar.

A wasikar, Oshiomhole ta jaddada cewa saboda rashin jituwa da aka samu a tsakanin 'yan jam'iyya da barazanar tashe-tashen hankula kafin zaben fitar da gwanin, duka masu son tsayawa takarar sun gana a otel din City King da ke Gusau domin cimma matsaya.

Ya ce bayan doguwar tattaunawa, sun cimma matsaya bisa sharuddan dokokin zabe da kundin tsarin jam'iyyar ya fitar da jerin sunaye kuma wakilan jma'iyya sun yi na'am da shi.

Kwamared Oshiomhole ya ce gudanar da zaben fitar da gwani ba shi kadai ba ne hanyar da ake bi wajen tsayar da dan takara, kamar yadda dokokin zabe suka shimfida.

Ya ce a jadawalin zabe da hukumar INEC ta fitar, ya bai wa jam'iyyu zuwa ranar 18 ga watan Oktobar 2018 ta aika da sunayen 'yan takararta.

Ya ce a matsayinsu na jam'iyya suna bin duka hanyoyin da suke da su wajen ganin su fitar da gwanayen da za su tsaya takarar gwamna da 'yan majalisun jiha da na dokoki a jihar Zamfara.

Rikicin siyasa a Zamfara dai ya kara zafi ne bayan da Gwamna Abdulaziz Yari ya sanar da goyon bayansa ga kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris, a matsayin wanda zai gaje shi.

Wannan ne ya sa wasu daga cikin masu sha'awar takarar gwamnan a jam'iyyar APC su takwas da suka hada da mataimakin gwamnan Ibrahim Wakalla da kuma Ministan tsaro Mansur Dan Ali suka hade kai domin yakar gwamnan na Zamfara.

Sau biyu anashirya zaben fitar da gwanin a jihar, amma sai a soke shi saboda rikicin siyasa tsakanin bangarorin jam'iyyar a jihar.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment