Saturday, 13 October 2018

Ashe Buhari ya taba dukawa ya gaishe da Atiku?

Wani tsohon na hannun damar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan watau Rino Omokri ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taba dukawa ya gaishe da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.


Omokri ya saka wannan hoton da ake gani a kasa wanda dai ga dukkan alamu Buharin ba Atikun ya ke gaidawa ba, amma Rino da yake yayi kaurin suna wajan sukar gwamnatin shugaba Buhari ya hakikance akan hakan.

No comments:

Post a Comment