Tuesday, 16 October 2018

'Ashe dalolinnan sadakin 'yarshine yake karba ba cin hanci ba'

A yayin da ake tsaka da badakalar zargin gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da karbar cin hancin daloli daga masu kwangila, wani sanatan PDP ya bayyana cewa yana da labari daga majiya me karfi cewa kudin sadakin 'yarshine aka bashi ba cin hanci ba.


Sanata Ben Murray Bruce ne yayi wannan ikirari ta shafinshi na dandalin Twitter inda yace, an sanar dani daga majiya me karfi cewa ba cin hanci mutumin ke karba ba. Dalolin da aka ga yana karba a cikin bidiyon sadakin diyarshi ne da ya aurar a farkon shekararnan. Ku daina neman magana.

No comments:

Post a Comment