Saturday, 20 October 2018

Atiku be da fahimta, bazai iya mulkar Najeriya ba>>Obasanjo

A wani faifan bidiyo da ya bayyana a shafukan sada zumunta wanda ya nuna cewa an dauki bidiyonne kusan sati daya kamin shiryawar Obasanjo da Atiku, an ga Obasanjon ana hira dashi inda ya bayyana dalilin da yasa Atiku ba zai iya mulkar Najeriya ba.


Obasanjo ya bayyana a cikin bidiyon cewa, Atiku mutum ne wanda bashi da fahimta domin yayi-yayi ya koyamai yanda ake gudanar da mulki lokacin yana mataimakinshi amma ya kasa fahimta.

Yace, Atiku be da burin zama mataimakin shugaban kasa, shine a wancan lokaci yayi shawarar cewa ya kamata su kawo sabon mutum ba tare da lura da kwarewarshi a iya mulki ba da fatan cewa shi Obasanjon zai dorashi akan hanya yanda daga karshe zai iya gadarshi.

Obasanjo yace ya rika baiwa Atiku aiki sosai-sosai ta yanda har saida Atikun ya fara kosawa, yace, yana sane yayi hakan dan ya gogar da Atikun a iya gudanar da mulki.

Ya kara da cewa, daya gama nuna mai yanda ake gudanar da mulkin cikin kasa sai kuma ya fara aikashi yana wakiltarshi a tarukan kasashen waje dana majlisar dinkin Duniya.

Yace, amma Atikun fa akwai lokuta da dama da yake yanke hukuncin da bai dace ba ace jagora yana yankewa ba, kuma ya gayamai ya gyara amma abin ya faskara.

Obasanjo yace da ya lura Atiku bazai fahimci yanda ake gudanar da mulki ba sai kawai ya hakura ya kyaleshi.

No comments:

Post a Comment