Wednesday, 17 October 2018

Atiku ya baiwa wanda gobarar bututun mai ta ritsa dasu taimakon miliyan 10

A wani yanayi na nuna tausayawa ga iyalan da gobarar bututun mai da ta faru a jihar Abia ta rutsa dasu, dan takarar shugaban kasa karkshin jam'iyar PDP, Atiku Abubakar ya basu tallafin naira miliyan 10.

A wata sanarwa da me magana da yawun tawagar kamfe din Atikun ta fitar tace, mataimakin Atikun, Peter Obine ya wakilceshi inda ya kai ziyara jihar ta Abia ya kuma jajantawa wadanda lamarin ya rutsa dasu, kamar yanda Punch ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment