Wednesday, 17 October 2018

Atiku ya bayyana yanda zai canja Najeriya daga zama matattarar talauci ta Duniya

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana dabarar da zai yi amfani da ita wajan warware matsalar kasancewar Najeriya hedikwatar talauci da ta yi karkashin mulkin shugaba Buhari.Atikun ya bayyana hakane ta dandalinshi na safa zumunta inda yace, A karkashin mulkin Buhari, Najeriya ta zama matattarar mutane mafiya talauci a Duniya. Domin canja wannan abu sai mun karfafawa mata da matasa gwiwa. Dan haka na dauki alkawarin idan Allah ya yadda mutanen Najeriya suka zabeni shugaban kasa, kashi 40 cikin dari na mukarrabaina zasu zama matane da matasa.

No comments:

Post a Comment