Saturday, 13 October 2018

Atiku ya kada Buhari a kuri'ar jin ra'ayin jama'a

A jiyane muka ji labarin yanda jaridar Daily Trust ta gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a akan wa zasu zaba tsakanin Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na shekarar 2019?Ko da a jiyan dai Atiku ya yiwa Buhari fintin kau inda ya nunka kusan sau uku kuri'ar da Buhari ya samu. A lokacin da muka ji labarin jiya ana ci gaba da kada kiri'unne.

Ya zuwa safiyarnan, Buhari na da kuri'a sama da dubu 3 yayin da shi kuma Atiku ke da sama da dubi 8.

No comments:

Post a Comment