Friday, 12 October 2018

Atiku ya kayar da Buhari a wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da wata babbar jaridar kasarnan ta gudanar

Jaridar Daily Trust ta shafinta na dandalin Twitter ta baiwa masu bibiyarta damar gudanar da zaben jin ra'ayinsu akan wa zasu zaba tsakanin Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na shekarar 2019 me zuwa?


Jaridar ta bukaci idan mutum na son Atiku ya danna Like idan kuma Buhari yake so yayi Retweet.

Sakamon zaben zuwa lokacin rubuta wannan rahoto ya nuna cewa masu son Atiku sun ninka masu son Buhari da kuri'u sama da 2000.
No comments:

Post a Comment