Sunday, 7 October 2018

Atiku ya lashe zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na PDP

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da aka gudanar a jihar Rivers.


Jaridar Thisday ta tabbatar da hakan a rahotonta na yau.

Kamin wannan lokaci dai gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ne ke kan gaba da kuri'u amma Atiku ya zo ya zarceshi.

Har yanzu dai PDP bata bayyana waye ya lashe zaben a hukumance ba.

No comments:

Post a Comment