Thursday, 11 October 2018

Atiku ya shiga ganawar sirri da Obasanjo

Dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Olusegun Obasanjo, ya isa gidan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.


Atiku wanda ya samu nasara a zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP bayan ya lallasa sauran yan takara 11 a Fatakwal. Ya zo neman goyon bayan tsohon maigidansa wanda ya bayyana adawa da shi tun bayan rabuwarsu.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya isa gidan Obasanjo misalin karfe 1:12 na rana tare da shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, da shugaba yakin neman Atiku, Otunba Gbenga Daniel.

Alhaji Atiku Abubakar ya kasance mataimakin shugaban kasa lokacin da Obasanjo ke shugaban kasa daga shekarar 1999 zuwa 2007. Amma sunyi hannun riga sanadiyar zargin rashawa da kasar Amurka ta yiwa Atiku a shekarar 2006.

Saboda haka, Obasanjo ya lashi takobin cewa ba zai taba goyon bayan Atiku a takarar neman kujeran shugaban kasa. Hakazalika, ya janye goyon bayansa daga shugaba Muhammadu Buhari

Suna cikin ganawar a yanzu da muke kawo muku rahoton.

Atiku Abubakar ne babban wanda ake ganin zai iya takawa Buhari mulki a zaben shugabancin kasan 2019.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment