Saturday, 13 October 2018

Atiku zai ji kunya a cewar Shugaba Buhari

Fadar Gwamnatin Najeriya ta ce Obasanjo zai ji kunya da shi da dan takarar Shugabancin Kasar na jam’iyyar PDP, domin Shugaba Buhari bai girgiza ba da goyan bayan da ya baiwa Atiku Abubakar a lokacin da ya ziyarci Obasanjo a Abeokuta.


Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana goyan bayan takarar Atikun ga zaben Shugabancin Najeriya a zaben kasar na shekara ta 2019.

Mai taimakawa Shugaba Buhari kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a hirar su da Kabir Yusuf wakilin mu a Abuja.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment