Wednesday, 24 October 2018

Ba ni da niyyar ficewa daga Jam'iyyar PDP>>Ekweremadu

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya karyata rahotannin da wasu ke yadawa na cewar yana shirin ficewa daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).


Duk da cewar baya Najeriya a halin yanzu, Ekweremadu ya yi amfani da shafin sada zumuntarsa ta Facebook domin tabbatar wa duniya matsayarsa a siyasance a safiyar yau Laraba.

Gogagen dan siyasar ya ce Allah ne kaddara abinda zai faru da mutum a rayuwa amma a halin yanzu yana nan a jam'iyyar PDP.

Sai dai The Cable ta ruwaito cewar wasu na kusa da Sanatan sun bayyana cewar baya ji dadin yadda jam'iyyar na PDP ke 'amfani da mutane kana tayi watsi da su ba'.

Wata majiyar kuma ta ce Ekweremadu bai ji dadin yadda babu wanda ya tuntube shi a yayin da kan batun zabin Peter Obi a matsayin mataimakin dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar.

Har ila yau, jam'iyyar PDP ba ta zabi Ekweremadu a cikin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar ba duk da cewa mai gidansa, Bukola Saraki wanda bai dade da dawowa PDP ba shine aka nada shugaban kwamitin yakin neman zaben.

Wata majiyar ta kuma ce jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tana zawarcin mataimakin shugaban majalisar amma bai amince ba saboda kada ya rasa goyon bayan da ya ke samu daga yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Legit.ng.

No comments:

Post a Comment