Tuesday, 2 October 2018

Ba ni kadaine ban yi bautar kasa ba>>Inji Ministan Buhari

Tsohon ministan sadarwa na Shugaba Buhari da ya ajiye mukaminshi dan yaje jiharshi ta Oyo tsayawa takarar gwamna, Adebayo shittu wansa kuma jam'iyyar APC ta hanashi tsayawa takara saboda bai yi bautar kasa ta NYSC ba bayan kammala karatun Jami'a, yace bafa shi kadaine baiyi bautar kasar ba.

Shittu ya bayyana hakane ga manema labarai yau, Talata, kamar yanda jaridar The nation ta ruwaito, yace APC bata mishi adalci ba hanashi tsayawa takarar da tayi ba kuma babu inda yake a doka cewa idan mutum bai yi bautar kasa ba a hanashi tsayawa takarar gwamna ba.

Ya kara da cewa, idan ma hakane ai ba shi kadaine be yi bautar kasar ba.

Ya karkare da cewa ya daukaka maganar hanashi tsayawa takarar zuwa kwamitin gudanarwar jam'iyyar na kasa kuma yana kira garesu da su duba wannan batu da idon basira dan gujewa wargajewar jam'iyyar tasu ta APC.

No comments:

Post a Comment