Thursday, 11 October 2018

'Ba za mu amince da albashin naira dubu 24 ba'

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun nuna rashin gamsuwarsu game da matakin gwamnatin kasar na gabatar da naira dubu 24 a matsayin mafi karancin albashin ma'aiktan kasar.


A ranar Laraba ne dai ministan kwadago na kasar Chris Ngige, ya shaida wa manema labarai cewa bayan tattaunawa da gwamnatocin jihohi, gwamnatin tarayya ta amince da Naira dubu 24 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata.

Hakan dai na zuwa ne bayan da aka koma teburin tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayyar kasar da kuma kungiyoyin kwadago, wadanda suka yi wani yajin aikin gargadi mako biyu da suka wuce.

Comrade Nasir Kabir, shi ne sakataren tsare-tsare hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa ULC a Najeriya, ya kuma shaida wa BBC cewa, su fa ana su bangaren sun dauki batun matakin da gwamanatin ta dauka game da mafi karancin albashin a matsayin wasan yara.

Don haka su sam ba za su taba amincewa da wannan kudi ba, domin tun farko ba haka suka yi da gwamnati ba.

Sakataren tsare-tsaren ya ce, idan har gwammnati ta gaza biya musu bukata a kan albashin, to akwai matakai da za su dauka, da suka hadar da sake tafiya yajin aiki, sannan kuma duk inda suka san akwai ma'aikatansu a ko ina a fadin kasa, to za su janye su daga wajen.

Comrade Nasir, ya ce 'Yakamata fa gwamnati ta sani cewa, idan fa aka ce ba bu ma'aikaci to fa ba bu gwamnatin ma kanta, don haka ma'aikatan nan fa su ne gatan gwamnatin'.

Comrade din ya ce, da farko sun cimma matsaya da jami'an gwamnati inda aka roki kungiyoyin kwadagon da su hakura mafi karancin albashi ya koma naira dubu 30, to amma su ba su amince da hakan ba ma.

Sakataren tsare-tsaren tsare-tsaren hadaddiyar kungiyar kwadago ta Najeriyar, ya ce yakamata fa gwamnati ta sani cewa ' Kananan ma'aikata na cikin kunci da wahala fa, don haka idan aka ce za a yi karin da bai taka kara ya karya ba me aka yi ke nan?'.

Don haka matukar gwamnati ba ta saurari koken talakawa da kananan ma'aikata ba, to Inn sha Allahu za su yi wa gwamnati yaren da ta ke so, na janye ma'aikatansu daga ma'aikatun gwamnati'.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment