Sunday, 28 October 2018

"Ba zamu sake siyar wa Saudiyya makamai ba">>Inji shugabar Jamus saidai Faransa tace hakan ba adalci bane

Shugabar gwamnatin Jamus,Ankela Merkel ta bayyana cewa, kasarta ba za ta sake siyar wa Saudiyya makamai ba.


Merkel ta yi wannan bayanin a wani taron manema labarai da ta shirya da firaministan kasar Czech,Andrej Babish a birnin Prag,inda ta ce kisan da aka yi wa dan jarida Jamal Khashoggi babban rashin imani ne,kuma ta bayyana ra'ayinta kan wannan lamarin ga sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdul-Aziz ta wayar tarho.

Shugabar ta Jamus ta kara da cewa,"A nan gaba Tarayyar Turai za ta kafa gimshikan sabuwar alakar da za ta kulla da Saudiyya.A matsayinmu na Jamusawa mun yanke shawarar dakatar da siyar wa Saudiyya daidai da harsashi daya, har sai ta fito fili don bayyana ainahin abin da ya afku da Khashoggi".

Tun watan Disamban bara ya zuwa yau, bayan kasar Aljeriya,Saudiyya ta kasance ta biyu a jerin kasashen da suka fi sayen makamai daga Jamus.

"Kin siyar wa Saudiyya makamai,zalunci ne"

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce,matakin da wasu kasashen Yamma suka dauka bayan kisan Khashoggi na dakatar da siyar wa Saudiyya makamai,zalunci ne,saboda babu abinda ya hada mutuwar dan jaridan da kuma kasuwancin makamai.

Macron ya furta wannan kalaman a wani taro da ya halarta a Bratislava,babban birnin kasar Slovakya.

Emmanuel Macron ya yi ganawarsa ta karshe da ministan harkokin wajen Austria, Karin Kneissl,inda ya ce bayyana a karara cewa,kin siyar wa Saudiyya makamai "Babban zalunci ne".

A farko dai Macron ya sanar da cewa, ya gana da sarkin Saudiyya,Salman Bin Abdul-Aziz,inda ya ce masa: "Yana bakin cikin yadda aka yi wannan kisan na rashin imani".

Bugu da kari,Macron ya bayyana wa Sarki Salman cewa:

"Kare hakkin fadar baki ga 'yan jarida na daya daga cikin muhimman hakkokin kasa.Faransa ba za ta taba yi kasa a gwiwa ba wajen warware bakin zaren wannan matsalar gaban kotun kasa da kasa".

A ranar 20 ga watan Oktoban bana,Saudiyya ta sanar wa duniya dan jarida Khashogi ya mutu a ofishin jakadancinta da ke Santambul.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment