Monday, 15 October 2018

Babban laifin da Buhari yayi da yasa dole a canjashi da Atiku>>Buba Galadima

Tsohon na hannun damar Buhari wanda tuni suka raba gari, Buba Galadima ya bayyana babban laifin da shugaba Buhari yayi wanda yasa dole 'yan Najeriya su canjashi da wani shugaban.

Buba Galadima ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja na bude wata kungiya me suna EPA kamar yanda jaridar Guardian ta ruwaito.

Buba Galadina ya bayyana cewa idan akwai mutumin da ya tallata Buhari tun daga shekarar 2002 zuwa yanzu to shine, idan kuwa bai zo na daya ba to zai zo na biyu, to yanzu dai ya tabbata Buhari ya gaza akwai bukatar a canjashi.

Ya gaza wajan samar da tsaro, babu tausayi a tattare dashi ana ta kashe mutane amma ko ya kai ziyara garuruwan da abin ya shafa wane irin shugabane wannan? , ga yunwa a gari, Buba Galadima yace a addinin musulunci idan dabba ta kwana da yunwa a mulkinka to sai Allah ya tambayeka ballantana dan Adam.

Ya kara da cewa ya goyi bayan Kwankwaso kuma duk da be ci zaben fidda gwani ba shine ya fi dukkan 'yan takarar karbuwa a lungu da sako na Najeriya amma dandai kawai a kawar da Buhari a gwada wani ya kamata a gwada Atiku a gani, shima kuma idan bai yi abinda ake so ba to za'a iya canjashi.


No comments:

Post a Comment