Wednesday, 31 October 2018

Bamu da shirin fara yin lemu da Wiwi>>Kamfanin Coca-cola

A kwanakin bayane muka ji cewa kamfanin Coca-cola zai fara amfani da ganyen wiwi wajan yin lemu inda lamarin ya dauki hankulan mutane sosai ganin cewa shine kusan kamfanin yin lemu na daya a Duniya.


Sabon rahoton CNN ya bayyana cewa kamfanin na Coca-cola yace a yanzu bashi da niyyar yin amfani da wiwi wajan yin lemun, sabanin rahotannin da aka ji a baya.

Me kamfaninne ya bayyana haka a gurin  wani taro da aka yi jiya, Talata.

No comments:

Post a Comment