Monday, 15 October 2018

Bamu fitar da sunayen manyan mutane 50 da aka hana fita kasashen waje ba>>Fadar shugaban kasa

Me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu yace, basu fitar da sunayen manyan mutanen kasarnan 50 da sabuwar doka ta hana su fita kasashen waje ba saboda shari'ar da ake musu a kotuna.


Garba ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewa, basu fitar da sunayen mutnen ba kuma basu da niyyar fitar dasu.

Ya kara da cewa an saka dokarne saboda samu a yi shari'a yanda ya kamata kuma idan mutum kudinshine za'a mayar mishi da kayanshi amma idan ba nashi bane, na al'umma ne to za'a mayar da su baitulmani.

Ya kuma ce mafi yawancin tuhune-tuhumen da akewa mutanen suma zuwa suka yi suka iske anayi dan kuwa sun wuce shekaru 10 ana yin su.


No comments:

Post a Comment