Sunday, 7 October 2018

Ban ce wa El-Rufai ya wa Shehu Sani Kiranye ba>>Shugaba Buhari

Fadar shugaban kasa ta hannun me magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu ta musanta cewa ta amshi wata wasika da wasu kafafen watsa labarai suka wallafa cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya aika mata inda yake tunawa shugaban kasar da maganar da suka yi ta cewa, Shugaba Buhari ya baiwa gwamnan umarnin yi wa Sanata Shehu Sani kiranye saboda rashin biyayyar da ya ke wa shugaba Buhari.


Fadar tace bata samu wata wasika irin wannan ba kuma shugaba Buhari tunda yake be taba cewa a yi wa wani dan jam'iyyar APC hukunci akan kin yi mishi biyayya ba, musamman ma Sanata Shehu Sani.

Shugaban ya ce yana kira ga jama'a da su yi watsi da wannan wasika dan babu kanshin gaskiya a cikin bayanan da ta kunsa.

A wasikar dai an ruwaito Gwamna Malam Nasiru El-Rufai na Kaduna yana wa shugaba Buhari tuni akan wani umarni da ya bashi na ayi wa sanata Shehu Sani kiranye wai akan rashin biyayya da yake wa shugaban.

Bayyanar wannan wasika dai ta saka wasuwasi kala-kala a zukatan mutane.

No comments:

Post a Comment