Sunday, 14 October 2018

Bana Shan giya ko shan taba kuma na daina harkar mata>>Atiku

A wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na TVC News da wani shafin Instagram ya wallafa, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa tuni ya daina bin mata.


Me hirar dashi ta tambayeshi cewa, kasan a Afrika akan ce idan mutum baya shan taba ko giya to yana bin mata, kai wanne kake yi? Sai Atikun ya bayar da amsar cewa baya shan taba kuma baya shan giya sannan ya daina bin mata.

Me hirar dashi ta sake tambayarshi cewa, shin ka iya soyayya kuwa, kasan cewa matanka sun fi saninka fiye  da kowa.

Sai ya bayar da amsar cewa, Eh na iya soyayya domin bana jin kunyar sumbatarsu, rungumar (matana) a bainar jama'a.

No comments:

Post a Comment