Tuesday, 16 October 2018

Banda tafiye-tafiye wane ci gaba Buhari ya kawowa Najeriya?>>Ummi Zeezee

Tauraruwar fina-fina Hausa, Ummi Zeezee ta bayyana irin abubuwan ci gaba da shuwagabannin da suka gabata a kasarnan suka kawo wa mutane inda tace, Babangida ya kawo jami'an kula da hanya, Obasanjo ya kawo EFCC, ICPC da GSM, 'YarAdua ya yiwa tsageran Naija Delta afuwa, Jonathan ya kawo katin zabe na dindindin da BVN.


Ummi ta kalubalanci masoya Buhari da su gaya mata wane irin ci gaba ya kawowa kasarnan? Tace ita dai tasan yana yawan tafiye-tafiye kamar matukin jirgin sama 

No comments:

Post a Comment