Saturday, 6 October 2018

Barkwanci: Haduwar 'yan sanda da direba

POLICE BA KYAU!!!
Wai wasu 'yan sanda ne suka tare wani driver. Ga yadda hirar tasu ta kasance:
POLICE: "Ina takardun mota?"
DRIVER: "Ga su"
POLICE: "Ina Driver's Licence?"
DRIVER: "Ga shi"Komai dai aka tambayi driver sai aga yana da su. Sai can suka ce...
POLICE: "Kai uban waye zaka dinga yawo kai daya. Idan ka mutu waye zai kai gawarka gida?"
DRIVER: "Ai ba ni kadai nake yawo ba. Manzon Allah (S.A.W) yace akwai wata addu'a wacce idan kayi Mala'iku dubu ne ke biye da kai suna gadin ka duk inda zaka, kuma nayi addu'ar kafin na fito daga gida.
POLICE: "AlhamdulilLah, Mala'iku dubu a
wannan 'yar karamar Motar!!To kayi OVER LOAD muje office za kayi bayani"
Marubutanhausa.com

No comments:

Post a Comment