Friday, 19 October 2018

Barkwanci: Tsakanin Wani da baya jin hausa sosai da matan wani gida

Wani mutum ne da baya jin hausa sosai yaje gidan matan aure inda 'yar uwarshi ke zaune da mijinta, gidan na kullene, da yaje sai ya kwankwasa, biyu daga cikin matan dake kusa sai suka matsa kusa da kofar suka tambaya, wanene?.

Sai ya amsa musu da cewa nine.

Sai suka tambaya wa kake nema?

Sai ya basu amsa da cewa mutum daya.

Nana kuwa suka runtuma da gudu dakunansu suka rufe.

No comments:

Post a Comment